EXECUTIVE SUMMARY IN HAUSA
Matsayin Dā na Κasa da Kasa
Bincike a kan tasiri, bidi’a, barazana, da ingantar da aiki tare na kafofi watsa labarai a kasashen Latin America, Kudancin-gabas na Asiya, da Afirka.
ABOUT US
This report was created by
thanks to support from
with additional support from
Takaitawa na Mussamman
Yayinda anoban kullewar ko’ina saboda korona ya bazzu ko’ina a duniya a farawar shekara 2020, sai kudaden tallace-tallace suka haura, sa’an nan masannan sha’anin labarai suka ja wa mutane kunne cewa wannan yanayin zai jawo abin da ake ce a turance: “extinction-level event” ga kungiyoyin labarai – wato abu ne wanda zai kawar da su.
Saboda mun ga yadda wannan yanayin zai shafi kafofin watsa labarai na gargajiya masu zaman kansu ne ya sa muka yi aiki tare da Sembra Media, har muka shiga bincike mai zurfi a farawar shekara 2021 domin mu ga yadda wadannan sabobin shiga kafofin watsa labarai suka yi a wannan lokacin, da kuma mene ne ya canja tun farkon bincikenmu a 2016.
Mun ji dadi yayinda muka tarar da cewa, yawancinsu daga 200 zuwa sama a cikin kafofin watsa labarai na gargajiya wadanda aka hada da su a cikin wannan binciken ba su yi rashin kudi sosai kamar yadda tsofafi masu kafofin watsa labarai suka yi ba. A karshe bayan binciken mu sai muka gane cewa sabobin nan ba su dogara a kan tallace-tallace ba, ban da haka kuma, tallafawa ga kafofin watsa labarai a shekara 2020 ya karu.
A farkon bincikenmu na Matsayin Dā na Kasa da Kasa, mun yi hira da masu kasuwanci a kafofin watsa labarai na gargajiya guda 100 a kasashe Argentina, Brazil, Colombia, da Mexico. A cikin wannan ruhoton, hade da hiran da muka yi da wadannan wurare 100 a kasashe Latin Americ, mun kara ruhoto na kasashe guda takwas, inda muka yi hira da shugabanan kafofin watsa labarai guda 49 a Afirka daga: Ghana, Kenya, Nigeria, da South Africa; da guda 52 a Kudancin Asiya: daga Indonesia, Philippines, Malaysia, da Thailand.
Tare da tawagar masu bincike guda 23 daga kasashensu, cikin jagorancin shugabanan yankunansu, mun yi hira a yarurukan wuraren a kowace kasa. Kowane hira ya kai sa’o’i 2-3 kuma kunshi da tamboyoyi guda 500 wadanda sun shafi fannin yadda labarai da yadda ya shafe su, ‘yancin kafofin watsa labarai, da tsarewa rayukan masu aikin watsa labarai, da hanyoyin shigan kudi da yadda ake kashe kudi, tsarin tawaga da yadda suke ji, da yadda ake amfani da kafofin watsa labarai musamman na yau da kullum na zamani, da dai na’ura da bidi’a.
Kamar yadda ake tsamani, an sami bambance-bambance tsakanin kafofin watsa labarai a yankunan Afirka, Kudancin-gabas na Asiya, da LatinAmerika, wanda mun hada a cikin wannan ruhoton. Amma abin da ya fi ba mu mamaki yayinda muke dudduba wadannan binciken da muka tattara, sai muka ga abubuwan da sun yi kama da juna tsakanin kungiyoyin nan masu watsa labarai musamman yayinda kowanensu yana kokari ya sa ido a kan al’ummansu da kuma yadda suka tsara abin kwatanci game da kasuwancinsu a wannan fannin watsa labarai wadanda za su yi tare.
Ko da yake yawancinsu suna gudanar da ayyukan ba da isashe kasafin kudi ba, amma duk da haka suna da tasiri mai kai labari idan an kwatanta nauyin tasirin da yawan tawagar da suke da shi da kuma kudaden da suke da shi. Yawancinsu sun gwaninta a aikin jarida a fannin bincike da tara labarai, kuma fiye da 50% sun sami lambar yabo daga kasashensu har ma daga kasashen waje saboda aikinsu.
Matsayin Dā na Kasa da Kasa yana nan a madadin bincike mafi zurfi da mafi fadi wanda an taba yi game da yanayin kafofin watsa labarai na kasashe a Latin America, Kudancin – gabas na Asiya, da Afirka. Game da yawancin abubuwa masu yawa kafin anoban koronan nan, abin da muka gane shi ne akwai garwayar barazana masu yawa da kuma ci nasara a kan abubuwan da ba mu sani tun dā ba.
Kafofin watsa labarai a wannan binciken wadanda suka kafa su mutane ne wadanda suka ba da kansu da duka zukatansu, wadanda suke a shirye su fuskance gwamnanti masu ci hanci, da ‘yan kasuwa masu hada kai cikin zamba, musamman na kasashe waje duk da rashin kudinsu. Yawancinsu sun sa ayyukan biyan bukatunsu a layi – har ma a bakin rayukansu.
Amma wannan ruhoton ba wai kukan neman taimako ga wani kungiya kafofi watsa labarai wadanda suke cikin matsalla ba ne – ko kadan – saboda yawanci wadanda suka kafa su mun tattauna da su, kuma ba su yi magana game da neman taimako ba ko kadan.
Manufanmu a wadannan shafofi masu biye shi ne mu fitar da wadanan ‘yan wasa a fannin kafofi watsa labarai a fili don kowa ya san su a kuma san muhimmincin abin da suke yi. Yawancin kafofin watsa labarai na kasa da kasa a wannan binciken sun ba da labarai wadanda suna da ainihin abubuwan da za su shafi duiniya gaba ki daya. Wadannan abubuwa sun shafi abubuwa kamar tsarewa abubuwan da suke fuskanta kawarwa daga fuskar duniya, jagoranci ayyukan da za su rage bambance-bambance tsakanin maza da mata, da kuma tilasta shugabanan gwamnati masu cin hanci su bar kujerunsu cikin wulakanci.
Muna rarraba abin da muka tarar saboda duka shugabanan kafofin watsa labarai sun dace ga taimakonmu domin su sami tsarewan da ya dace da su sa’ad da suna yaki ne da ikokin masu yawa ne. Ban da haka kuma, muna rarraba abin da muka tara saboda mu sami goyon baya a fannin kudade domin mu iya taimaki kafofin watsa labarai masu zaman kansu don su iya yi wa al’ummansu hidima – da karfafawa demokradiya – na shekaru masu zuwa nan gaba.
Yin aiki a tsakiyar barazana ko’ina da kuma kawo hari
Wadannan sabobin shiga a kafofi watsa labarai suna fuskance matsalolli masu yawa iri na farawa, amma sukan yi aikinsu a yanayin da sauran ‘yan kasuwanci sukan yi mamaki yadda wadannan sabobi kafofi watsa labarai suke yi – daga hari na zanen gizo zuwa hari na ido da ido.
Ko’ina a yankunan ukun nan, 51% na kungiyoyin kafofi watsa labarai a cikin wannan binciken da muka yi, sun ce mana sun fuskanci hari daga zanen gizo – wato intanet – kuma 40% sun ce sun fuskance barazana saboda aikin da suke yi – kullum a kowane mako, wani lokacikowace rana.
Barazana daga zanen gizo ya zama abu na yau da kullum har yawancin kungiyoyn da muka tattauna da su sun ce sun zama abin barazana ta wurin kowane irin hari na zanen gizo – musamman kafofi yanayin rayuwa na yau da kullum.
Yadda kafofin watsa labarai na kasa da kasa suka sami kudaden shiga a shekara 2019 da 2020
Don fahimtar yadda kafofin watsa labarai na kasashe suke yi kafin anoban korona, mun yi muhimman tambayoyi masu zurfi game da hanyoyin samun kudaden shiga da kuma hanyoyin kashe kudaden a shekara 2019 da 2020.
Daga farko zuwa karshe na wannan ruhoton, mun yi amfani da abin da muka samu daga 2019 don kada mu ci karo da wadansu abubuwan da ba su shafi abin da muke bincike ba saboda anoban COVID-19. Ban da haka, duk inda muka hada da abubuwan da muka samu daga 2020, mun yi haka ne kawai a inda muka lura cewa akwai bambance-bambancen da sun fita a fili sosai.
Muna so a lura cewa, ba duka kafofin watsa labarai ba ne sun yarda su amsa tambayoyinmu game da hanyoyin kudaden shiga da fannin kudade, wadansu sun ki su amsa, duk da cewa mun yi musu alkawari da tabbaci cewa wannan tsakaninmu ne da su. Saboda wannan, ruhoton da muka bayar a fannin kudade yana nan a kan abin da muka samo daga 141 a ciki 201 na shugabanan kafofin watsa labarai wadanda muka tattauna da su ne. Don mu iya kwatanta abin da muka samo, mun canja kudaden shiga da kudaden fita zuwa dalla na Amerika (US Dollars) muna amfani da tsakaicin yadda ake canja kudi a shekarar ruhotonmu.
Daga wannan kafan watsa labarai da wancan a duka yankunan ukun nan a cikin wannan binciken, wuraren da sun fi samun kudaden shiga sune: tallafi, tallace-tallace, hidimomin shwarware, hidmomi na ciki, kudaden shiga daga masu karatu, a wannan oda a duka shekarun.
|
|
|
|
| |||||
| 28.08% | 30.75% | $48,258 | $63,597 | |||||
| 23.32% | 20.81% | $27,903 | $27,323 | |||||
| 11.96% | 10.26% | $17,664 | $27,770 | |||||
| 8.28% | 6.86% | $10,492 | $14,066 | |||||
| 8.27% | 6.49% | $23,180 | $21,834 |
* Duka wadannan an hada su tare da sauran wuraren da suka kunshi yankuna ukun nan.
- Tallafofi: Wannan ya kunshi duka kudaden da aka samu daga kungiyoyi masu zaman kansu, da ‘yan jari masu taimako, da hukumomi masu zaman kansu, kamar Google da Facebook, har ma da kudin tallafi daga kungiyoyin gwamnantin kasashen waje da kungiyoyin gwamnati na kasarmu.
- Kudaden Shiga: Wannan ya kunshi duka sauran wuraren samun kudin shiga wanda aka ba da ruhotonsu, wato hade da Google Adsense, da tallace-tallace, da tsarin gabbaobin aidarwa, da sakonin da aka tallafa, da tallace-tallace na gargajiya, da tallace-tallacen da wadansu kungiyoyi suka yi, da ayyukan ma’aikata.
- Duka kudaden shiga daga Hidimomin Ciki: Wannan ya kunshi kudaden shiga daga ayyuka na ciki – wato na wadatta, abubuwa na musamman wadanda aka shirya wa gabobin watsa labarai, abubuwan da aka shirya wa wadanda ba na gabobin watsa labarai ba, da zane-zane ko tsarin hidimomi na fasaha.
- Duka kudaden shiga daga Masu Karatu: Wannan ya kunshi kudaden neman sashi a jeridanmu, ko kudin neman zaman memba, ko kudin jarida, ko kyautayin da mutane suka bayar, – ko mutum shi kadai ko kungiyoyi, da kuma kudade daga sayar da tikiti da dai sauransu.
Wannan kudaden tallafi ya tsaya a matsayinsa saboda ya zama hanyar samun kudaden shiga mai muhimminci a tsakanin kafofin watsa labaran da muka bincika a Latin Amerika a shekara 2016. A lokacin da aka ba da ruhoton tallafi, kafofin watsa labarai 16% ne kadai aka sa a cikin farkon bincikenmu.
A shekara 2019, goyon bayan tallafi a duka yankuna ukun nan a wannan binciken, sun kunshi 28% na jimlar duka kudaden shiga, har ya yi girma zuwa 31% a shekara 2020. Tsakaicin kudaden tallafi ga kafa watsa labarai ya yi girma daga $48,000 a shekara 2019 har zuwa fiye da $63,000 a shekara 2020. Goyon bayan tallafi ya ma fi a Latin Amerika.
A cikin tattaunawa na daya da daya, mun ji labari cewa masu ba da kyauta da masu tallafi damuwarsu yana karuwa kullum cewa kafofi watsa labarai masu zaman kansu sun fara sa yawan karfinsu a kan tallafi, mu ma wannan yanayin yana damunmu. Ko da yake, akwai dalilin ba da gaskiya cewa wannan kasuwancin ba da kyauta da goyon baya yana daya daga cikin abubuwan da suka taimake wadannan kafofin watsa labarai su yi tsaya daram a lokacin “hatsarin koronan” nan.
Don a sa abin da muka samo a inda yakamata, abu mai muhimminci ne mu lura cewa, saboda suna da kasafin kudi kadan don farawa, tallafi kome kankantanta zai taimaka sosai.
Fiye da 60% na kafofin watsa labarai na kasa da kasa a wannan binciken sun ba da ruhoto cewa ba sa samu kudin da ya kai $50,000 gaba ki daya a kudaden shiga a shekara 2019,kuma 8% sun ba da ruhoto cewa ba su sami kudaden shiga ba gaba ki daya, wato sun dogara a kan wadanda suka ba da kansu ne kawai.
Amma ba wai suna nan kanan ba. Ko’ina a yankuna ukun nan a shekara 2019, fiye da 36% sun ba da ruhoton kudaden sihiga wanda ya fi $100,000, sa’an na 15% sun ba da ruhoto matsakaicin shekara wanda ya fi million $1.
Ban da haka kuma, mun tarar da cewa, kusa 25% sun kare shekara 2019 da riba bayan da suka cire kudaden da sun kashe.
Kudaden tallace-tallace su ne na biyu a hanyar mafi muhimmincin samun kudaden shiga, sa’an na kudaden shiga na matsakaici ga kowane kungiya bai canja sosai ba a kimani $28,319 a shekara 2019, da $27,323 a shekara 2020.
Don mu kara fahimta yadda kafofin watsa labarai a kowane matsayi suna gina tsarin kasuwancinsu, sai muka fitar da tsarin sunaye 30 na hanyoyin kudaden shiga, wanda muka bincika dalla-dalla a Sura na “Ginawa Tsarin Kasuwanci” wanda a turance ake ce da shi: ‘Building Business Models’.
Mun dade muna jagoranci yadda za sami hanyoyin kudaden shiga dabam-dabam domin samun zaman kai da yin aiki tare, amma bayna da mun kwatanta yawan hanyoyin da kowane kafofin watsa labarai suke da shi, da kuma yaya ne wadannan hanyoyin sun taimake kowanensu a fannin kudaden shiga na kowace shekara, sai muka tarar cewa samun hanyoyi kudaden shiga daga biyu zuwa shida shi ne mafi kyau na samun kudaden shiga.
Wadanda suka ba ruhoto fiye da shida ahanyoyin kudaden shiga, ba lallai ba ne sun fi sauran samun kudaden shiga, sai muka gane cewa, wannan matsalla ce ga yawanci ‘yan kasuwa wato: yawancinsu sukan dauki shirin ayyuka da yawa a lokaci daya wanda zai iya hana su samun ci ma burin abin da suka shirya.
Tawagai masu fasihai dabam-dabam za su iya samu kudaden shiga fiye da sauran
Abu mafi muhimminci daga wannan binciken da muka yi daga farkon binciken kungiyoyi kafofin watsa labarai shi ne yadda suka hada mutum daya mai goninta da kwazo a fannin kasuwanci a cikin tawagarsu.
A cikin wannan bincike wanda ya fi wancan fadi, mun tarar cewa wannan ya shafi duka yankuna ukun nan. Wadanda suka ba da ruhoto cewa suna da wani a cikin ma’aikatansu mai karbar albashi sun yi riba sau shida har zuwa tara a karbar kudaden shiga a shekara 2019 fiye da wadanda ba su da mai karbar albashi a cikinsu.
A wannan lokaci kuma, mun kuma tambaye su ko nawa ne suke biyansu, muka tarar cewa albashi na matsayi a sha’anin gina kasuwanci yana fara daga $200 zuwa $2,000 a wata, wato na ko’ina a duniya a tsakaicin shekara waje $733.
Bayan da muka duba yananayin biyan ma’aikaci mai kwazo cikin neman kudaden shiga, da kuma albashi mai araha a wuraren nan, sai muka gani cewa, sa kudi a cikin kasuwanci da a kan ma’aikata shi ne muka ba da shawara cewa ya fi kyau.
A cikin sauran abubuwan da muka tarar, kungiyoyin kafofi watsa labaran da suke da shugabanai wadanda suka mika kai ga fasaha ko bidi’a sun ba da ruhoto cewa suna samun kudaden shiga sau uku fiye da sauran – ko ma ba su da mai sayar da kaya a tawagarsu.
Yawan mata amma masu shi kadan ne mata
Daya daga cikin abubuwan da sun fi burge mu daga farkon ruhotonmu na Matsayin Dā na Kasa da Kasa shi ne cewa, mata suna da wakilci wajen 38% a cikin wadanda suke da kafofi watsa labarai a cikin duka masu kafa kungiyoyin watsa labarai bayan da muka tattauna da mutane 100 a Argentina, Brazil, Colombia da Mexico.
Wannan abin da muka tarar ya babbar nasara ce saboda ya nuna cewa mata masu yawa suna da ofishi ko kujerar matsayi teburin mai kafa wadannan sabobi kafofin watsa labarai fiye da gidajen jeridu da gidajen telebishan a kasuwancinsu, inda mata masu shi yana kasa da 1%.
A wannan binciken, mun tarar cewa duka masu kafa kamfanonin da muka bincike guda 201, mata sun kunshi 32%, ko da yake ya bambanta bisa ga yanki zuwa yanki, kuma ya fi kasawa a Afirka.
Ban da haka kuma, mun tayar da cewa mutane 25% sun ce daya daga cikin masu kafa kungiyoyin nan, yana wakilci karama hukuma na al’uma a kasarsu ne: kusa 30% a Latin America, 25% a Kudancin-gabas Ashiya, da 20% a Afirika.
Wane ne yakamata ya karanta wannan ruhoton
Muna rarraba wannan ruhoton abin da muka samu da manufan taimako masu kasuwanci a kafofin watsa labarai, amma masu gidajen watsa labarai na gargajiya su ma za su iya mora daga wannan binciken, yayinda kasuwanci na kafofin watsa labarai a hankali suna kawar da na gargajiya.
Muna da sani cewa a hankali cikin natsuwa muna wallafa wannan ruhoton da zatto za mu wallafa shi nan gaba kuma a “Matsayin Dā na Kasa da Kasa” ba da dadewa ba a tarihin kafofin watsa labarai na kasa da kasa. Yayinda suna kokari su yake labaran karya da kuma kokarin yin aikin ba wa la’ummansu labarai masu kyau, dole ne su lura suka kuma jimre da yanayin da anoba korona ya bari a baya musamman a fannin kasuwanci a kasashensu, yayinda suke kuma fuskance barazana da hare-hare iri-iri.
Fattanmu shi ne, abubuwan da muka fitar da su, da shawarwaren da muka bayar, da abubuwa mafi ka’idar da muka bayar a wannan ruhoto zai karfafa gwiwar masu kafofin watsa labarai, da shugabansu, da masu tallafinsu, masu shehun kimmiya, da dai wadanda suna da kishin taimakonsu domin su girma, su karfafa su don su iya ba wa al’ummansu labarai masu kyau a hanyoyin da za su karfafa demokradiya na kasashensu.